rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Gabon

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gabon za ta sake fadawa rikici- Ping

media
Jagoran 'yan adawar Gabon, Jean Ping STEVE JORDAN / AFP

Madugun ‘yan adawar Gabon da ya sha kayi a zaben shugabancin kasar Jean Ping ya gargadi cewa, kasar za ta sake tsindima cikin wani sabon rikici matukar kotun kasar ta ki amicewa da bukatarsa.


Ping ya yi gargadin ne bayan ya shigar da kara a kotun saboda zargin hukumomin kasar da yin murdiya a sakamokon zaben, wanda ya bai wa Ali Bongo nasara.

Mr. Ping na bukatar kotun da ta amince da bukartasa ta sake kidayan kuri’un da aka kada a cikin watan jiya.

Kotun dai na da kwanaki 15 don yanke hukunci game da karar da Ping ya shigar mata.