Isa ga babban shafi
Tanzania

An samu asarar rayuka sakamakon girgizar kasa a Tanzania

Wata girgizar kasa mai karfin maki 5.7, da ta auku a kasar Tanzania ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutane 13, da raunata wasu 203.

Yankin Bukoba a Tanzania da girgizar kasa ta aukawa
Yankin Bukoba a Tanzania da girgizar kasa ta aukawa
Talla

Girgizar kasar ta auku ne a lardin Kagera da ke arewa maso yammacin kasar.

Kwamishinan da ke kula da yankin, Deotus Kinawilo ya ce yanzu haka an fara sallamar wasu daga cikin wadanda suka samu raunuka.

Rahotanni sun ce anji motsawar girgizar kasar a kasashen Ruwanda, Burundi, Uganda da kuma Kenya saboda karfinta.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.