rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Gabon

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

AU za ta Sa ido kan Shari'ar korafin zabe da ke Gaban Kotu

media
Shugaban Gabon Ali Bongo Ondimba STEVE JORDAN / AFP

Kungiyar Kasashen Afirka ta AU ta ce za ta tura masu sa ido dan taimakawa kotun kolin kasar kan korafin da shugaban 'yan adawa Jean Ping ya yi na zargin shugaba Ali Bongo da tafka magudi a zaben da ya gabata.
 


Majalisar tsaro da wanzar da zaman lafiya ta kungiyar ta bukaci tura masu sa ido daga kasashen da ke Magana da Faransanci dan taimakawa jami’an kotun.

Kungiyar kasashen Turai ta ce akwai kura kurai kan yadda aka gudanar da zaben a Yankin Haut-Ogooue.