Isa ga babban shafi
Burundi

Masu bicinke na MDD sun futar da jerin sunayen wandada suka ci zarrafin Al'umma

Ma’aikantan Majalisar Dikin Duniya dake gudanar da bicinke kan kasar Burundi sun futar da sakamakon farko kan kasar dake nuna cewa akwai hannun wasu mayan jami’an Gwamnati da suka azzabtar da fararen fula a rikicin siyasa na baya baya nan.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Burundi
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Burundi STR / AFP
Talla

Bicinken dai ya maida hankali ne kan batutuwan da suka shafi azzabtarwa,fyade a kasar ta Burundi.

Mai Magana da yahu ita hukumar dan Afrika ta kudu Christof Haynes ya sheidawa gidan rediyon faransa sashen faransanci da cewa sun tattara sheidu tareda nadar muryoyin jama’a da suka sheida cewa sun ganewa idanu su ta yada wasu mayan jami’an Gwamnati suka bayar da umurni wajen gallazawa yan kasar.

Wadanan rahotani daga ita hukumar bicinke bai baiwa Gwamnatin kasar mamaki ba a cewar shugaban hukumar leken asirin kasar Janar Alain Guillaume, jami’in ya bayyana cewa kungiyoyi na kokarin shafawa gwamnatin kasar kashin kaji.

Janar din ya karasa da cewa Burundi kasa ce mai bin doka da oda ,kawar da ido a kokarin wasu tsiraru dake kokarin wargaza batun tsaro tareda gudumuwar wasu yan siyasa bai dace ba.

A karshe Hukumar bicinke da ta futar da wannan sakamako ta saka sunayen wasu membobin Gwamnati da suka hada da Shugaban hukumar leken asirin kasar,babban hafsan sojan kasar da wani jami’in dake aiki a fadar shugaban kasar ta Burundi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.