Isa ga babban shafi
Amurka-Lafiya

Zuckerberg zai taimakawa wajen magance cututukan yara kanana

Makirkirin dandalin sada zumunta na Facebook Mark Zuckerberg tare da matarsa Priscilla Chan sun yi alkawarin bayar da kimanin Dala Biliyan Uku domin bincike tare da magance cututuka, musamman wadanda ke addabar kananan yara.

Mark Zuckerberg, wanda ya samar da shafin sada zumunta na Facebook
Mark Zuckerberg, wanda ya samar da shafin sada zumunta na Facebook REUTERS/Stephen Lam
Talla

Ana sa ran amfani da kudaden wajen kafa cibiyoyin bincike na lafiya, saukaka samar da magunguna, sai kuma maida hankali kan lura da lafiyar kwayoyin halittar jiki.
Yayin da yake jawabi a wajen taron gidauniyar Matarsa da ya gudana a birni San Fransisco na Amurka Zuckerberg ya ce kafin cimma wannan matsaya sun shafe shekaru suna tattaunawa da masana bincike a lafiya.

Dan haka a cewar Zuckerberg babban abinda za’a maida hankali kai a yanzu shi ne gayyato fitattun masana kimiyya da injiniyoyi da zasu jagoranci samar da cibiyoyin binciken da kuma na’urorin da za’a bukata.

Cibiya ta farko da za’a kafa mai suna Chan Zuckerberg BioHub, zata lakume dala miliyan 600, karkashin jagorancin masana kimiyya da injiniyoyi daga garin Stanford sai kuma jami’ar jihar Carlifornia duk da suke kasar Amurka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.