rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Barack Obama Wariyar fata

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Obama ya jagoranci bikin bude wani gidan tarihi bakar fata

media
Shugaban Amurka Barack Obama a bikin bude gidan tarihin bakar fata a Washington REUTERS/Joshua Roberts

Shugaba Barack Obama a karo na farko ya jagoranci bikin bude wani gidan tarihi na bakar fata a birni Washington. Gidan dake dauke da tarihin bakar fata a Amurka, an dai bayyana cewa a wannan wuri an ajiye kayyakin tarihi dake nuna jarumtakar bakar fata kama daga lokutan bauta na jahiliya zuwa lokutan da aka soma samun bakaken fata a harakokin yau da kullum a kasar ta Amurka.
 


Ana danganta bude wannan katafaren wuri da Shugaba Obama yayi kafin sauka daga mukaminsa na Shugaban kasar Amurka a watan janairu shekarar badi a matsayin nasara.