rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Gabon Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jean Ping ya bukaci sawa Gabon takunkumi

media
Jagoran adawa na kasar Gabon Jean Ping.

Jagoran 'Yan adawar Gabon Jean Ping yayi kira ga kasashen duniya da su kakabawa kasar takunkumi saboda abinda ya kira magudin zaben shugaban kasar da ya baiwa Ali Bongo wa’adi na biyu.


Ping ya bukaci kasashen duniya sun sanya takunkumin kan duk wani wanda ya taka rawa wajen magudin zaben, da kuma rufe asusun ajiyar kasar dake kasashen waje kana da hana shugabannin ta tafiye tafiye.

Sabon Firaministan kasar da aka nada Emmanuel Ngondet yace a shirye yake ya kafa gwamnatin hadin kai a karshen mako, inda ya bukaci Jean Ping ya shiga tattaunawa dan dinke barakar da aka samu.

Rikicin da ya biyo bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da ya nuna Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 50.