Isa ga babban shafi
Libya

EU ta tsawaita takunkumi kan shugaban Majalisar Libya

Tarayyar Turai EU ta kara wa’adin takunkumin da ta kakabawa shugaban Majalisar kasar Libya da kuma wasu ‘yan majalisun guda biyu, saboda kin goyon bayan gwamnatin hadakar kasar da ke samun taimakon majalisar Dinkin Duniya.

REUTERS/Stringer
Talla

Shugaban Majalisar Aguila Saleh da sauran yan majalisu biyu, Khalifa Ghweil da Nuri Abu Sahmein, sun jagoranci majalisar Libyan kada kuri’ar rashin amincewa da gwamnatin Libya a watan Agusta, lamarin da yasa tarayyar turai ta haramta musu shiga nahiyar tare da kwace kadarorinsu da ke nahiyar.

A cewar tarayyar turan hakan koma baya ne ga kokarin daidaita zaman gwamnatin hadakar da ake yi a kasar.

EU ta kara da cewa matakin na Saleh da mukarrabansa barazana ce ga kokarin da ake na samun zaman lafiya a kasar tun bayan fadawarta rikici sakamakon hambarar da tsohon shugaban kasar Mu’ammar Gaddafi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.