An kaddamar da cibiyar tunawa da Sankara
A birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, a wannan lahadi aka kaddamar da wani gagarumin shiri domin tunawa da tsohon shugaban kasar Thomas sankara, wanda aka kasher anar 15 ga watan okotoban 1987.
Wallafawa ranar:
A wurin wannan biki na yau wanda ya samu halartar baki ciki da wajen kasar, kamar tsohon shugaban Ghana Jerry Rawlings, an kafa wata cibiya da za ta rika yada manufofi na salon juyin-juyin hali da kuma kishin Afirka, kamar dai yadda marigayin ya rika yadawa a lokacin rayuwarsa.
A ranar 2 ga watan oktoba kimanin shekaru 32 da suka gabata, tsohon shugaban ya gabatar da wani jawabi wanda a cikin yake fatan kwato Afirka daga ‘yan mulkin mallaka, to sai dai makonnin biyu bayan hakan ne aka bindige shi tare da binne gawarsa a gaggauce.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu