rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Congo Brazaville Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane 14 sun rasa rayukansu a Congo

media
Wasu mutane mazauna birnin Brazaville da suka tsere daga gidajensu sakamakon barazanar tsaro

Akalla mutane 14 aka tabbatar da mutuwar su sakamakon wani hari da ake zargin tsoffin yan tawayen Congo Brazaville da kaiwa cikin wani jirgin kasa.


Kakakin 'yan sanda Jules Monkala Tchomou, yace cikin wadanda suka rasa rayukansu, a lokacin harin da ‘yan tawayen Ninja Nsilolulou suka kai, harda yara kanana da kuma sojoji guda biyu.

Ita dai kungiyar Ninja Nsiloulou ta gwabza yakin basasa sau biyu a kasar, kuma tana karkashin wani malamin addinin Krista ne da ake kira Frederic Bintsamou, wanda mabiyan sa ke kira manzo.

Tun a watan Aprilu wannan shekara rundunar sojin kasar ta Congo ta girke jami’anta a kudancin birinin Brazaville bayan harin da ‘yan a’addan suka kai inda suka kashe mutane 17.

A shekara ta 2003 jagoran ‘yan tawayen, Bitsango ya taba rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu da gwamnatin kasar.