Isa ga babban shafi
Nijar-Jamus

Merkel ta fara ziyara Mali da Nijar

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta soma ziyarar kwanaki uku a Afrika inda ta fara ziyarar a Mali kafin ta je Nijar da Habasha. Shugabar za ta kuma gana da shugabannin kasashen Najeriya da Chadi a Berlin bayan ta kammala ziyarar a Afrika.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel Reuters
Talla

Merkel zata tattauna da shugabannin kasashen uku na Afrika kan batun ‘Yan ci rani da ke kwarara zuwa Turai da kuma batun yaki da ta’addanci.

Bayan ta kammala ziyara a Habsha ne kuma zata gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Chadi Idriss Deby a birnin Berlin na Jamus kan yaki da ta’addanci.

Tuni dai Jamus ta ce za ta bude sansanin Soji a Nijar domin taimakawa dakarun Majalisar Dinkin Duniya da ke fada da ‘Yan tawaye a Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.