Isa ga babban shafi
Habasha

Habasha ta musanta amfani da karfi fiye da kima kan masu zanga zanga

Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn ya musanta zargin da ake yiwa ‘yan sandan kasar na yin amfani da karfi fiye da kima kan masu zanga-zanga a kasar.

Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn
Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Jawabin Firaministan na zuwa bayan da sama da mutane 50 suka rasa rayukansu a wata zanga zanga da ta auku a yankin Oromia da ke nuna rashin goyon aya ga gwamnatin Habasha.

Gwamnati dai tayi zargin cewa wasu marasa kishin kasar sun kambama yawan wadanda suka mutu sakamakon zanga zangar, yayinda a gefe guda ta zargi kasashen Eritrea da Masar da hannu wajen assasamata rikici a kasar.

Firaminista Desalegnyayi alkawarin kaddamar da bincika zargin tare da hukunta wadanda aka samu da aikata laifuka.

Sama da shekara guda kenan kasar ta Habasha ke fama da tashe tashen hankula a yankin Oromia da ke kasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.