Isa ga babban shafi
Najeriya

Wasu Jiragen kasashen waje za su daina jigila a Abuja

Wasu jiragen kasashen waje da ke jigila a Najeriya sun sanar da wani sabon tsarin dakatar da jigila a birnin Tarayya Abuja saboda matsaloli na raguwar fasinjan wanda ya samo asali daga faduwar darajar Naira.

Jirgin Kamfanin Emirates
Jirgin Kamfanin Emirates REUTERS
Talla

Kamfanin Emirates na Daular Larabawa ya sanar da cewa daga ranar 30 karshen wannan watan na Oktoba zai dakatar da jigila ta hanyar Abuja.

Haka ma jirgin Kenya Airways zai dakatar da jigilar ne a Abuja daga ranar 15 ga watan Nuwamban gobe.

Amma Kamfanonin jiragen biyu sun ce zasu ci gaba da jigilar a birnin Lagos.

Emirate ya sanar da cewa sau daya ne jirginsa zai sauka a Lagos sabanin sau biyu a rana.

Man da jiragen ke sha ne a yanzu ne ya yi tsada saboda faduwar darajar Naira, sannan matsalar ta fi shafar jirage ne domin da Naira fasinjan ke sayen tikiti shiga jirgi. Kuma babu tabbas kan yadda Naira ke ci gaba da faduwa akan dalar Amurka.

Najeriya na fuskantar koma bayan tattalin ariki sakamkon faduwar farashin mai a kasuwar duniya wanda kasar ke dogaro.

Matsalar ta haifar da karancin dala a Najeriya lamarin da ya dakatar da aikin kamfanoni da dama tare rasa ayyukan yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.