rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

CAF Gabon Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hukumar kwallon kafa ta Gabon ta kori mai horar da yan wasan kasar

media
Jadawalin wasannin gasar cin kofin Afrika na Gabon shekara ta 2017 cafonline.com/Youtube

A kasar gabon Hukumar kwallon kafar kasar ta raba gari da mai horar da kungiyar dan kasar Fotugal Jorge Costa.
Kungiyar da aka sani da sunan Les Pantheres wacce ke karbar bakucin gasar cin kofi Afrika na shekarar mai zuwa ta 2017, koci dan kasar Fotugal ya kasa samu nasarori a wasannin da kungiyar Gabon ta buga a baya.
 


A cewar wata majiya bai dace a ce kasar ta Gabon dake shirya gasar ci kofin Afrika ta ci gaba da tafiyar hawainiya, ta buga wasa da Moroko ranar 8 ga watan oktoba wasar da aka tashi ba kare bi damo, dangane da neman tikiti zuwa gasar cin kofin Duniya.

Banda haka koci duk da yake kasar Gabon ke shirya gasar cin kofi Afrika bai halarci babban bukin futar da jadawalin wasannin da aka yi a birnin Libreville bisa shugabancin hukumar kwallon kafar Afrika ta Caf, ana kuma zargin sa da nuna son rai da bi umurnin wasu yan wasa mai makon yi aiki da konyar sa wajen atasaye.

Jose Antonio Garrido mataimakin sa dan kasar Fotugal ne mai horar da kungiyar Gabon na wucin gadi yayinda wata majiya ke tabbatar da cewa hukumar kwallon kaffa na cikin tattaunawa domin dinke Baraka kafin soma gasar cin kofin Afrika a kasar.