Isa ga babban shafi
Congo

'Yan adawa na son Congo ta fice daga ICC

Wasu manyan jami’yyun adawa a kasar Congo sun bukaci gwamnatin kasar ta fice daga karkashin kotun hukunci kan manyan laifuka ta kasa da kasa, ICC da ke Hague.

Masu zanga zanga a birnin Brazzaville
Masu zanga zanga a birnin Brazzaville
Talla

Jam’iyyun da suka hadar da 'Patriotic Front' da kuma '2020 Awakening Movement', sun jagoranci sama da mutane 300 gudanar da zanga zangar lumana a babban birnin kasar Brazzaville.

A cewar masu zanga zangar, tsarin kotun ICC ya sabawa kundin tsarin mulkin Congo, wanda ya haramtawa kasar mika duk wanda ya nemi mafaka a wajenta zuwa ga wata hukuma ko kasar waje.

A watan da ya gabata ne itama kasar Gambia, ta yanke shawarar ficewa daga karkashin kotun ICC bisa zarginta da fifita jagororin kasashen yamma, yayinda ta ke hukunta na nahiyar Africa.

Tuni suma kasashen Namibia, Burundi da kuma Africa ta Kudu suka sanar da daukar makamancin matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.