Isa ga babban shafi
Benin

An saki dan kasuwar da aka zarga da safarar hodar Iblis a jamhuriya Benin.

A jamhuriyar Bénin, dan kasuwar nan Sébastien Ajavonya ya samu saki, bayan da kotu ta bayyana shakkunta kan zargin da ake yi masa cewa, an gano hodar iblis a daya daga cikin kwantinar kayan da kamfaninsa ya yo oda da kasar Brazil.

Sébastien Ajavon bayan goyawa takarar  Patrice Talon a zagaye na 2 na zaben shugabancin kasar Benin na 2016.
Sébastien Ajavon bayan goyawa takarar Patrice Talon a zagaye na 2 na zaben shugabancin kasar Benin na 2016. PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Talla

Kotun hukumta laifuka ta birnin Kotono ce ta sallameshi tare da mutane ukun da ake tsare da su tare.

Dan kasuwar, da ya zo na uku a zaben shugabancin kasar jamhuriyar ta Benin da ya gabata, ya share tsawon kwanaki 8 a tsare, sakamakon gano hudar iblis mai nauyin kilo gram , 18 da aka yi a cikin kwantinar kamfaninsa a ranar 28 ga watan octoba da ya gabata, al’amarin da ya ce ana kokarin bata masa suna ne kawai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.