Isa ga babban shafi
Morocco

Matsalar dumamar yanayi ta fi yin illa ga kasashen Afrika

Rahotan da Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar a taron sauyin Yanayi da ake gudanarwa a birnin Marrakesh na Morocco ya ce kashi 4 cikin 10 na kasashen da akafi samun gurbatar yanayi sun fito ne daga Afrika.

Manufar taron shine yadda za a aiwatar da yarjejeniyar Paris ta canjin yanayi da aka amince a bara.
Manufar taron shine yadda za a aiwatar da yarjejeniyar Paris ta canjin yanayi da aka amince a bara. REUTERS/Youssef Boudlal
Talla

Rahoton wanda aka fitar a zauren taron canjin yanayi da ake gudanarwa a Afrika yace matsalar dumamar yanayi ta fi yin illa ga kasashen Afrika.

Rahoton ya ce kasashen na Afrika sun fi fuskantar Matsalolin da dumamar yanayi ke haifarwa da suka hada fari da ambaliya da iska mai tafe da tsawa da tumbatsar teku.

Sannan rahoton ya zayyana kasashe 10 da mtaslar dumamar yanayin ta fi shafa a Afrika da suka da Mozambique da Malawi da Ghana da Madagascar.

Sannan akwai kasashe irinsu Haiti da Myanmar da Philippines da Vietnam da Thailand da Bangladesh da Pakistan da kuma Honduras da suka fuskanci matsalolin da dumamar yanayin ya haifar.

Rahoton ya ce kusan mutane rabin miliyan suka mutu saboda dumamar yanayi a tsakanin 1996 zuwa 2015

Babbar manufar taron da ake gudanarwa a morocco dai ita ce yadda za a aiwatar da yarjejeniyar Paris ta canjin yanayi da aka amince a watan disemban bara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.