Isa ga babban shafi
Japan

Japan za ta tura dakaru Sudan ta kudu

Gwamnatin Kasar Japan ta amince da wani shirin gaggawa na tura sojojin da za su yi aikin samar da zaman lafiya a Sudan ta kudu, wanda shi ne irinsa na farko da sojojinta za su yi aiki a wata kasa tun bayan yakin duniya.

Sojojin kasar Japan
Sojojin kasar Japan REUTERS/Issei Kato/Files
Talla

Matakin ya biyo bayan dokar da Majalisar kasar ta amince da ita bara domin fadada ayyukan Japan a kasashen waje, wanda yanzu zai kai ga tura sojojin daga ranar 20 ga watan Nuwamba.

Firaminista Shinzo Abe ya shaidawa Majalisar kasar cewar Sudan ta kudu ba za ta iya samarwa kanta tasro ba, saboda haka ya zama wajibi a taimaka mata.

Kasar Kenya da ke da tarin sojoji a Sudan ta kudu ta fara janye su tun bayan rahotan samun kwamandan ta da laifin sakaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.