Isa ga babban shafi
Masar

Kotu ta soke hukuncin kisa kan Morsi

Wata kotu a kasar Masar ta soke hukuncin kisa da aka yankewa hambararren shugaban kasar Mohammed Morsi na jam’iyyar “Yan uwa Musulmi”.

Tsohon shugaban kasar Masar Mohamed Morsi
Tsohon shugaban kasar Masar Mohamed Morsi AFP PHOTO / STR
Talla

A watan Yunin shekara ta 2015, aka yankewa Morsi hukuncin, bayan samunsa da hannu kan fasa gidajen yari a sassan kasar, a lokacin da ake gudanar da tarzomar nuna kin jinin gwamnatin Hosni Mubarak a shekara ta 2011.

Bayan juyin juya halin a Masar ne, Morsi ya dare shugabancin kasar bayan gudanar da zabe, sai dai a shekara ta 2013, Janar Abdel Fata al Sisi ya dare mulkin kasar bayan hambarar da gwamnatin Morsi, sakamakon zanga-zangar nuna kin jini da ya fuskanta a waccan lokacin.

Soke hukuncin kisa kan Morsi, ya fitar da shi daga fargabar fuskantar hukuncin kisa, sai dai har yanzu yana cikin kangin zaman gidan yari har kashi uku masu tsawon gaske.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.