Isa ga babban shafi
Najeriya

Amnesty ta zargi Sojin Najeriya da kashe 'Yan Biafra 150

Kungiyar Kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta zargi jami’an tsaron Najeriya da kasha masu fafutukar neman kasar Biafra sama da 150 daga bara zuwa bana. Amma rundunar sojin Najeriya ta karyata rahoton.

Masu neman kafa kasar Biafra a kudancin Najeriya
Masu neman kafa kasar Biafra a kudancin Najeriya AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Kungiyar ta yi zargin cewar, jami’an tsaron sun amfani da harsasai da kuma karfin da ya wuce kima wajen afkawa masu zanga-zangar.

Amnesty ta ce rahoton da ta fitar ya biyo binciken da ta gudanar da kuma hirarraki da mutane kusan 200 da hotuna da bidiyo kusan 200 da suka tabbatar da zargin.

Amma Rundunar Sojin Najeriya ta karyata rahoton kungiyar inda Kanal Usman Kukasheka ya ce babu gaskiya a rahoton da ya danganta a matsayin bacin suna ga sojin kasar.

Kanal Usman Kukasheka ya shaidawa RFI Hausa cewa babu wani lokaci da jami’ansu suka kashe adadin mutane kusan 150.

Kukasheka ya ce kungiyar Amnesty ta ki fadin barnar da masu zanga-zangar neman ‘yancin Biafra suka yi inda ya ce sun kashe ‘Yan sanda biyar a ranar 30 na Mayun bana tare da salwantar da dinbin dukiyoyin jama’a

02:47

Kanal Usman Kukasheka ya kartaya rahoton Amnesty kan Biafra

Bashir Ibrahim Idris

Kungiyar IPOB da ke fafutikar tabbatr da kasar Biafra ta ci gaba zanga-zanga tun kame daya daga cikin shugabanta Nnamdi Kanu a watan Oktoban bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.