Isa ga babban shafi
Senegal

Sall ya nisanta musulunci da ta'addanci

Shugaban Sengal Macky Sall wanda ke jagorantar taro karo na uku kan batun tsaro da zaman lafiya a nahiyar Afirka a birnin Dakar, ya nisanta addinin musulunci da ayyukan ta’addanci. 

Shugaban Senegal Macky Sall da tawagar shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a birnin Dakar
Shugaban Senegal Macky Sall da tawagar shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a birnin Dakar RFI hausa
Talla

Sall, wanda ke jawabi a gaban shugabanni da kuma wakilan kasashe a wannan taro, ya ce dole ne a himmantu wajen samar da ilimi ga matasa domin hana su fadawa a hannu masu tsatsauran ra’ayi ko kuma akida.

Taken taron na bana dai, shi ne yaki da tsatsauran ra’ayin kishin addini yayin da shugaban na Senegal ya bukaci taimakon kasashen waje, in da ya ce, nahiyar Afrika na bukatar kwararrun sojoji don yaki da masu ikirarin jihadi.

Mr. Sall ya koka kan rashin kwarewa a bangaren sojojin Afrika, abin da ya sa ya zama dole a karfafa su da kayan aiki da kuma horo.

Taron na zuwa ne a dai dai lokacin da kasashen yammacin Afrika da suka hada da Najeriya da Niger da Kamaru da Chadi ke fama da rikicin Boko Haram.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na daya daga cikin mahalarta taron wanda aka fara a jiya Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.