Isa ga babban shafi
Ghana

Zaben Ghana: John Mahama ya amince da shan kaye

Jagoran ‘yan adawa a kasar Ghana na jam’iyyar NPP, Nana Akufo-Addo ya samu nasara kan abokin takararsa shugaban kasar mai ci John Mahama.

Nana Akufo-Addo zababben shugaban kasar Ghana mai jiran gado
Nana Akufo-Addo zababben shugaban kasar Ghana mai jiran gado REUTERS/Luc Gnago
Talla

A daren Juma’a baturen hukumar zaben kasar, Charlotte Osei ya sanar da cewa Nana Akufo-Addo ya samu da kashi 53.8 na kuri’un da aka kada a zaben shugabancin kasar, yayinda John Mahama ya samu kashi 44.4 na kuri’un.

A wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na Twitter, Nana Akufo-Addo mai shekaru 72, ya ce shugaba Mahama ya taya shi murnar da yasamu a zaben shugabancin kasar, a wani kira da yayi masa ta wayar tarho.

Zalika a zabukan ‘yan majalisun da ya gudana tare da na shugaban kasar, jam’iyyar adawa ta NPP ce ta samu rinjaye.

Akufo Addo ya taba rike mukamin ministan harkokin waje na Ghana kafin daga bisani a nada shi Minsitan shari’ah na kasar a tsakanin shekarun 2001 da 2009.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.