Isa ga babban shafi
Burundi

Yunkurin magance rikicin siyasar Burundi ya gamu da cikas

Yunkurin kawo karshen rikicin siyasa da kasar Burundi ke fama da shi ya gamu da cikas, bayanda bangaren ‘yan adawa a kasar, ya zargi mai shiga tsakaninsu, wato tasohon shugaban Tanzania Benjamine Mkapa da karkata ga bangaren gwamnati.

Taron jama'a a yankin Nyakabiga dake makwabtaka da babban birnin Burundi Bujumbura, inda 'yan bindiga suka harbe wani mutum
Taron jama'a a yankin Nyakabiga dake makwabtaka da babban birnin Burundi Bujumbura, inda 'yan bindiga suka harbe wani mutum AFP Photo/Carl de Souza
Talla

A watan Maris da ya gabata, aka amince tsohon shugaban Tanzanian, ya jogaranci sulhu tsakanin gwamnatin Burundi da ‘yan adawa, yunkurin da kawo yanzu bai yi nasara ba.

A watan satumban da ya gabata, Majalisar Dinkin Duniya ta koka bisa karuwar tsarewa da kuma azabtar da ‘yan adawa a kasar, yiwa mata fyade, sai kuma bacewar wasu mutane da dama da har yanzu ba’a gansu ba, duk dai a sakamakon rikicin siyasar da kasar ke fuskanta.

Tuni dai gwamnatin kasar ta yanke alaka da jami’an kare hakkin dan’adam na Majalisar Dinkin Duniya, tare da ficewa daga karkashin kotun ICC, bayaga zargin kasashen yamma da yunkurin haifar da rikici a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.