rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Gabon Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

"Zaben Gabon na cike da kuskure-EU

media
Shugaban kasar Gabon Ali Bongo

Masu sa ido na kungiyar Tarayyar Turai EU, sun ce an tafka manyan kura-kurai a zaben shugabancin kasar Gabon da aka yi cikin watan Agustan da ya gabata, wanda aka ce Ali Bango ne ya yi nasara.


Sanarwar da ‘yan kallon na Tarayyar Turai suka fitar, na a matsayin ayar tambaya dangane da sahihancin wannan zabe da yanzu haka wanda ya sha kaye Jean Ping ke ci gaba da nuna rashin amincewa da sakamakonsa.

Sakamakon zaben shugabancin kasar ta Gabon ya nuna cewa Ali Bongo ya lashe zaben ne tazarar kuri’u 6000, sanarwar da ta haddasa tashin hankali da zanga zanga a sassan kasar tsawon kwanaki biyu, inda akalla sama da mutane 3 suka mutu, jami’an tsaro kuma suka kame mutane 800.