Isa ga babban shafi
Sudan ta kudu

An rike madugun ‘yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar

Rahotanni daga Afrika ta kudu sun ce hukumomin kasar sun tsare shugaban ‘Yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar dan ganin ba a bar shi ya koma gida dan tada tarzoma ba.

Madugun 'yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar.
Madugun 'yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar. REUTERS
Talla

Majiyoyin diflomasiya sun ce Afirka ta kudu ta dauki matakin ne dan ganin an magance rikicin Sudan ta kudu wanda tuni ya lakume rayukan mutane sama da miliyan guda.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Afirka ta kudu Clayson Monyela ya tabbatar da zaman Machar a kasar amma yace ba tilasta masa a ka yi ba ganin Afirka ta kudu kasa ce da ke shiga tsakani a rikicin.

Sabani tsakanin shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa kuma madugun ‘yan tawaye ya haifar da kazamin yakin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu biyu baya ga miliyoyin da suka rasa matsuguni.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.