Isa ga babban shafi
Burkina Faso

An kai wa sojojin Burkina Faso hari

Sojojin kasar Burkina Faso 11 ne suka rasa rayyukan su a wani kazamin hari da wasu yan bidinga suka kai kan wani barikin soja dake Nassoumbou kan iyaka da kasar da kasar Mali.

Sojojin kasar Burkina Faso
Sojojin kasar Burkina Faso RFI/Yaya Boudani
Talla

Maharan da aka danganta da zama mayakan Kungiyar jihadi dake dauke da makamai yawansu ya kai 40 sun kuma abkawa sojojin na Bukina Faso , da sanyin safiyar yau juma’a.

An share tsawon lokacin dai ana bata kashi da makamai ne, ‘yan ta’adan su yi nasarar kasha sojojin na Burkina Faso 11, a yayin da wasu guda 2 suka bata, kamar yadda kwamishinan yan sandan yankin Moahammed Dah ya sanar da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

Tun lokacin da lamarin ya faru ne dai, gwamnatin kasar ta Burkina Faso ta sanar da tura Karin sojojin a wannan yankin, domin bin sahun maharan da kuma karfafa matakan tsaron cikin da kan iyakokin kasar.

Wannan hari dai shi ne, irinsa na 2 da kai tsaye ya nufi dakarun sojan kasar ta Burkina Faso, dake fuskantar hare-haren mayakan jihadi, tun cikin watanni uku farkon shekara ta 2015

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.