Isa ga babban shafi
Gambia-Darfur

An soke ziyarar babban Hafsan sojin Gambia zuwa Darfur

Majalisar Dinkin Duniya da dakatar da babban hafsan sojin kasar Gambia Janar Badjie daga yunkurin da yayi na ziyartar sojin kasarsa da ke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Darfur na Sudan.

Babban Hafsan sojin Gambia Janar Badjie
Babban Hafsan sojin Gambia Janar Badjie
Talla

Matakin na zuwa a dai dai lokacin da gwamnatin Gambia karkashin Yahya Jammeh, ke cigaba da fuskantar matsin lambar mutunta sakamakon zaben shugabancin kasar da aka gudanar.

A dai ranar Talatar da ta gabata sojin kasar suka mamaye ginin hukumar shirya zaben kasar, bayan Jammeh ya ce ba zai amince da kayen da ya sha ba a zaben shugabancin kasar, duk da a baya a amince da hakan.

Wata majiyar zauren Majalisar Dinkin Duniyar ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, mamaye ginin hukumar shirya zaben Gambia da sojojin kasar suka yi, na daya daga cikin dalilan da yasa Majalisar daukar matakin hana babban hafsan sojin kasar kai ziyarar yankin na Darfur.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.