Isa ga babban shafi
Sudan

An kara wa'adin tsagaita wuta a Sudan

Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir, ya sanar da tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta na tsawon wata guda a fadan da dakarunsa ke yi da ‘yan tawaye a yankin Darfur. 

Shugaban Sudan Omar Hassan Al Bashir
Shugaban Sudan Omar Hassan Al Bashir Ashraf Shazly/AFP Photo
Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da rahotanni ke cewa wasu ‘yan bindiga sanye da kakin Soji sun kashe mutane kusan 10 a yankin na Darfur mai fama da rikici a jiya Litinin.

Tun a watan Oktoban 2016 ne, bangarorin biyu suka amince da tsagaita bude wuta a yankunan kudancin Blue Nile da Kordufan, amma har yanzu ana samun rikici a Dafur.

Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga sun bude wuta a Nertiti, yankin Darfur, in da suka kashe mutane 8 yawancinsu mata da aka bindige a cikin gida.

Tun a 2011 ne sabon fada ya barke tsakanin dakarun Sudan da ‘yan tawaye a Kordufan da Blue Nile, a lokacin da Sudan ta kudu ta balle daga kasar.

Amma tun a 2003 ake rikici a Darfur, in da kabilun Sudan da ba larabawa ba suka dauki makamai suna fada da gwamnatin al Bashir ta larabawan Sudan.

An dai dade ana kokarin sulhu domin samun zaman lafiya kuma wannan ne ya sa shugaban ya kara tsawaita tsagaita wuta a sakon sabuwar shekara domin bude kofar sasantawa da ‘yan tawayen a Darfur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.