Isa ga babban shafi
Senegal

An bai wa 'yan Senegal da ke waje kujeru a majalisa

Mahukuntan Senegal sun ce daga zabe mai zuwa za a bai wa ‘yan asalin kasar da ke zaune a waje, damar samun kujeru 15 a cikin zauren majalisar dokokin kasar.

Majalisar tarayyar Senegal da ke bienin Dakar
Majalisar tarayyar Senegal da ke bienin Dakar wikiwand.com
Talla

Wannan dai na nufin cewa ‘yan Senegal da ke rayuwa a kasashen waje, za su samu kashi 10 cikin 100 na yawan kujerun da ake da su a zauren majalisar.

Tuni dai majalisar dokokin kasar ta amince da wannan shiri, lura da muhimmancin da ‘yan kasar da ke zaune a waje ta fannin tattalin arziki, in da alkalumma ke cewa a kowace shekara suna turo kudaden da yawansu ya kai Dala milyan dubu daya da milyan 400 zuwa gida.

Senegal dai kasa ce da ke da yawan al’umma milyan 13, kuma akwai wasu dubban da ke rayuwa a kasashen Turai da suka hada da Faransa da Italiya da kuma Spain.

Wani dan majalisar dokokin kasar Moustapha Diakite ya ce, majalisar za ta kunshi wakilai 195 bayan karin kujeru 15 a zaben da za a yi nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.