Isa ga babban shafi
Ghana

An rantsar da Nana Akufo-Addo a Ghana

A yau assabar aka rantsar da sabon shugaba a Ghana Nana Akufo-Addo, wanda ya yi alkawarin kawar da rashawa da farfado da masana’antu a kasar. 

Sabon shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya karbi rantsuwar kama aiki
Sabon shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya karbi rantsuwar kama aiki REUTERS/Luc Gnago (
Talla

Akufo-Addo mai shekaru 72, wanda tsohon lauyan kare hakkin dan adam ne, ya karbi rantsuwar kama aiki a birnin Accra, wanda ya samu hallatar baki daga ciki da wajen kasar sama da dubu 6.

Daga cikin jawaban kama aiki da sabon shugaban ya gabatar akwai batu rage kudadden haraji da janyo hankali masu zuba jari daga ketare don farfado da tattalin arzikin Ghana.

Tun ranar Alhamis tsohon shugaba John Dramani Mahama ya yi jawabin bankwana ga alummar kasar, inda ya nuna ya yi na shi kokarin kuma zai sauka domin sabon shugaban kasar ya yi nasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.