Hissene Habre na Chadi zai daukaka kara
Tsohon shugaban Chadi Hissene Habre na shirin daukaka kara littini mai zuwa dangane da hukuncin dauri rai-da-rai gidan yari da Kotun Hukunta masu aikata laifukan yaki ta zartas masa a Darkar na kasar Senegal.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Hissene Habre mai shekaru 73 tun a watan mayu daya gabata aka zartas masa da wannan hukuncin.
A watan juli daya gabata Kotun ta nemi ya biya diyya na kudin Amurka Dala dubu 33 ga mutanen da aka azabtar a lokacin da yake mulki.
Shi dai Hissene Habre ya ki amincewa da wannan kotun wadda Kasar Senegal da Kungiyar Tarayyar Africa suka kafa domin sauraron tuhumar da ake masa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu