rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Zaben Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An yi zanga-zangar goyon bayan gwamnati a Nijar

media
Shugaban Jamhuriyyar Nijar Issoufou Mahamadou AFP/AFP

A jamhuriyar Nijar dubban mutane ne suka gudanar zanga-zangar nuna goyon baya ga shugaban kasar Issoufou Mahamadou wanda a kwanakin da suka gabata wasu kungiyoyin fararen hula da kuma ‘yan adawa suka gudanar da irin wannan zanga-zanga domin nuna rashin amincewa da salon mulkinsa.


Zanga-zangar ta jiya ta samu halartar dubban mutane kamar dai yadda jam’iyyun siyasa kusan 50 da ke marawa shugaban kasar suka bukaci a yi.

A zanga-zangar da suka gudanar a kwanakin baya, 'yan adawa da kuma kungiyoyin fararen hula sun zargin shugaban kasar Issoufou Mahamadou da gazawa a cikin mulkinsa, yayin da suka yi zargin gwamnatinsa da yada rashawa.