Isa ga babban shafi
COTE D'IVOIRE

Ouattara ya kore jami'an tsaro

Shugaban Cote d’Ivoire Alassane Ouattara ya tube babban kwamandan askarawan kasar Janar Soumaila Bakayoko, da shugaban rundar tsaro ta jandarma Gervais Kouakou Kouassi daga mukamansu, kwana daya bayan shawo kan boren soji da aka yi a birnin Bouake.

Shugaba Alassane Ouattara na Cote d'Ivoire
Shugaba Alassane Ouattara na Cote d'Ivoire © Handout / IVORY COAST PRESIDENCY / AFP
Talla

Har ila yau matakin ya shafi shugaban rundunar ‘yan sandan kasar Bredou M’bia inda aka tura dukkaninsu zuwa ritaya.

A ranar Juma'a ne dai sojoji suka hau titunan suna yin bore a Bouake, kafin daga bisani 'yan uwansu na bariki su mara musu baya, a sauran biranen kasar.

Sojoji sun kawo karshen bore ne bayan shugaban ya amince da biya musu bukatunsu wanda ya tayar da hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.