Isa ga babban shafi
Ivory Coast

Gwmnatin Ivory Coast ta sasanta da Sojoji dake bore

Sojan dake bore a kasar Ivory Coast sun cimma yarjejeniya da Gwamnatin kasar game da batun neman albashi mai tsoka da batun biya masu sauran bukatu.

Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara
Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

Babu dai karin bayani dangane da fasalin yadda aka sasanta, amma kuma majiyoyi na cewa  littini aka yi masu alkawarin samun hakkokin su.

Majiyoyin samun labarai a kasar sun bayyana cewa anyi ta jin rugugin harbe-harben bindigogi a wani barikin soja dake birnin Abidjan kafin warware takaddamar.

Bore da soja suka yi na tsawon kwanaki biyu sun yi ta harbe-harbe da razana jama’a daga barikin su dake Bouake, suna bukatar albashi mai tsoka da kuma mallakan gidaje.

Daga bisani boren ya bazu zuwa sauran barikokin sojan ciki har da na babban birnin kasar Abidjan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.