Isa ga babban shafi
Gambia

Amurka ta gargadi Jammeh kan mika mulkin Gambia

Amurka ta gargadi shugaban Gambia mai barin gado Yahya Jammeh, in da ta ce, yana wasa da damarsa ta mika mulki cikin ruwan sanyi ga Adama Barrow da aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben watan Disamba.

Yahya Jammeh ya ayyana dokar ta baci a dai dai lokacin da ake saran ya mika mulki ga Adama Barrow a gobe Alhamis
Yahya Jammeh ya ayyana dokar ta baci a dai dai lokacin da ake saran ya mika mulki ga Adama Barrow a gobe Alhamis MARCO LONGARI / AFP
Talla

Amurka ta gargadi Jammeh da ya ki amince wa da shan kayi game da abin da zai biyo baya matukar ya ki sauka a gobe Alhamis, ranar da wa’adinsa zai kare.

A wani taron manema labarai, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka, John Kirby ya ce, Jammeh na kokarin jefa Gambia cikin mummunan hali.

A ranar Jumma’ar da ta gabata ne, Amurka ta nuna goyon baya ga kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS dangane da daukan matakin da ya dace matukar Jammeh ya ki mika mulki kamar yadda doka ta tanada.

A gobe ne dai ya kamata a rantsar da Adama Barrow a matsayin sabon shugaban kasa da zai gaci Jammeh wanda ya shafe shekaru 22 akan madafun iko, yayin da ECOWAS da kuma kungiyar kasashen Afrika AU suka ce, za a daina mutunta Jammeh a matsayin shugaban kasa daga gobe Alhamis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.