Isa ga babban shafi
Gambia

MDD ta amince da matakin ECOWAS kan Gambia

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da matakain kungiyar kasashen yammacin Afrika, ECOWAS, na amfani da karfin soja wajen saukar Yahya Jammeh na Gambia da ya ki sauka daga karagar Mulki.

Shugabanni Afrika da ke shirin yakin Kawar da Yahya Jammeh daga mulki
Shugabanni Afrika da ke shirin yakin Kawar da Yahya Jammeh daga mulki SUNDAY AGHAEZE / AFP
Talla

Kasar Senegal ce ta gabatar da kudurin wanda ya samu amincewar dukkanin mambobi 15 na kwamitin tsaron.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya rawaito cewa tuni dakarun kasar Senegal sun kutsa cikin kasar ta Gambia, kamar yadda majiya mai karfi daga rundunar sojin ta Senegal ta tabbatar.

Tuni dai aka rantsar da Adama Barrow a Matsayin shugaban kasa a ofishin jakadancin kasar Gambia a Senegal.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.