Isa ga babban shafi
Kamaru

Jirgi ya fadi da sojojin Kamaru

Sojojin kasar Kamaru guda 4 sun mutu bayan faduwar jirgin da suke ciki a Bogo yankin arewa mai nisa a lokacin da suke tsara kai hari kan Mayakan Boko Haram. Wata majiyar soja ta ce cikin wadanda suka rasu har da Janar Jacob Kodji da wani Kanal.

Sojojin Kamaru da ke fada da Kungiyar Boko Haram ta Najeriya
Sojojin Kamaru da ke fada da Kungiyar Boko Haram ta Najeriya RFI/OR
Talla

Jami’in ya ce hafsoshin sojin na tafiya Yankin Bogo da ke Arewacin kasar ne lokacin da jirgin mai saukar ungulu ya fadi.

Janar Kodji ke jagoranci runduna 4 da ake yi wa lakabi da Emergence 4 da ke yaki da ‘Yan Boko Haram.

Majiyar ta ce Sojojin sun nufi dajin Waza ne domin yakar Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.