Isa ga babban shafi
ECOWAS-GAMBIA

Gambia: Sojojin ECOWAS za su bada tsaro na watanni 6

Kungiyar Kasashen yammacin Afrika ta ce sojojin ta da aka tura Gambia dan tabbatar da zaman lafiya za su kwashe watanni 6 suna aiki a kasar kamar yadda shugaban kasa Adama Barrow ya bukata.

Dakarun Ecowas za su bada tsaro na watanni shida a Gambia
Dakarun Ecowas za su bada tsaro na watanni shida a Gambia Photo: Carl de Souza/AFP
Talla

Shugaban gudanarwar kungiyar Marcel de Souza ya bayyana haka lokacin da ya ke jawabi ga jami’an diflomasiya kan halin da ake ciki a Gambia.

De Souza ya ce taron shugabanin rundunar sojojin kasashen Afirka ta Yamma zai yanke hukunci kan matakan da za a dauka wajen sake horar da sojojin Gambia.

Dangane da komawar shugaba Barrow gida, de Souza ya ce suna sauraron rahoto kan halin da ake ciki a Banjul kafin sanin lokacin da Barrow zai koma gida.

Yanzu haka dai majalisar Kasar ta soke doka ta bacin da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya ayyana a makon jiya kafin ya tsallake ya bar kasar.

Shugaban masu rinjaye a Majalisar, Fabakary Tombong Jatta, ya ce sauyin da aka samu ya sa Majlisar ta soke dokar.

Akalla mutane 76,000 suka tsere daga kasar dan kaucewa tashin hankali, yayin da Hukumar kula da 'Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla 8,000 sun koma gida yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.