Isa ga babban shafi
Gambia

Adama Barrow ya samu kyakkyawar tarba a Gambia

Dubban Mutane ne suka tarbi sabon shugaban kasar Gambia Adama Barrow wanda ya koma gida daga Senegal bayan ficewar Yahya Jammeh da ya kwashe shekaru 22 a karagar mulki. Dakarun kungiyar kasashen Afirka ta Yamma suka samar da tsaro ga sabon shugaban.

Shugaba Adama Barrow ya isa birnin Banjul na Gambia
Shugaba Adama Barrow ya isa birnin Banjul na Gambia RFI/Guillaume Thibault
Talla

Sanye da fararren Tufafi da Hula, Mista Barrow ya sauka a Gambia ne cikin matakan tsaro.

Tawagar Gwamnatinsa da manyan mambobin Jam’iyyarsa, na daga cikin wadanda suka tarbe shi bayan isowarsa tare da matansa biyu da ‘ya’ya.

Barrow ya zagaya ta wasu daga cikin titunan kasar a budadiyar mota yana dagawa daruruwan ‘yan kasar da suka yi layi a tituna hannu.

Kuma ya bayyana farin cikinsa da komawa gida, inda ya ce zai kafa sabuwar gwamnatin don fara aiki ba tare da bata lokaci ba.

An jima dai ana dakon dawowar Barrow Gambia wanda ya samu mafaka a Senegal sakamakon turjiya da Yahya Jammeh ya nuna na kin mika Mulki.

Komawar Barrow a yau Alhamis don tafiyar da kasar, zai bude sabon shafi a rayuwar al’ummar Gambia da suka shafe shekaru 22 karkashin mulkin tsohon shugaba Yahya Jammeh da ya sha kaye a zaben Disamban 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.