Isa ga babban shafi
Somalia-Kenya

Kungiyar Al-Shabab ta kashe Sojojin Kenya sama da 60

Sojoji sama da 60 ne suka rasa rayukansu sanadiyar harin da mayakan Al-Shabab suka  kai a kan sansanin sojin wanzar da zaman lafiya na AU da ke Somaliya.

Dakarun wanzar da zaman lafiya a wani wuri da mayakan Al-Shabab suka kai hari a bara.
Dakarun wanzar da zaman lafiya a wani wuri da mayakan Al-Shabab suka kai hari a bara. REUTERS
Talla

Mayakan sun kai harin ne a safiyar yau juma’a a barikin sojin mai suna Kolbiyow da ke karkashin ikon dakarun kasar Kenya masu aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia.

Daya daga cikin mayakan ne ya  soma tarwatsa kansa a lokacin da ya ke kokarin kutsa kai da mota a cikin barikin.

Jim kadan da fashewar bom na farko wasu daga cikin mayakan Al-Shabab da ke cikin shiri a sansanin sun afkawa barikin Sojojin  inda aka share wani lokaci ana barin wuta a tsakanin bangarorin biyu.

Daga bisani kungiyar ta Al-Shabab ta fitar da sanarwa inda a ciki ta dauki alhakin kai harin kan barikin da kashe sojojin fiye da sittin tare da kwace makamai da motocinsu  da dama.

Ikirarin da tuni rudunar Kenya da ke aiki a kasar ta Somaliya ta karyata.

Al-Shabab dai na kokarin wargaza yunkurin kasashen Duniya na tabbatar da zaman lafiya a kasar ta Somaliya ganin wannan shine karo na biyu cikin mako guda da ta ke kai irin wannan harin kan jami’an tsaro.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.