Isa ga babban shafi
AU- Summit

Kungiyar kasashen Africa na taron ta na watanni 6

Shugabannin  Kungiyar Tarayyar Africa na shirin zaben sabon shugaban hukumar kungiyar  a taron ta na watanni 6 da aka soma yi a yau Litinin a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma tana jawabi a wani taron kungiyar Tarayyar Africa
Uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma tana jawabi a wani taron kungiyar Tarayyar Africa www.au.int
Talla

Kasashen kungiyar 54 za su zabi sabon shugaba  kasancewar shugaban Hukumar mai barin gado Uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma ba ta neman wa'adi na biyu na shugabancin wannan Hukuma.

Yanzu haka dai akwai ‘yan takara 5 dake neman hawa kujeran na tsawon shekaru 4.

Ta kasance mace ta farko data shugabancin Hukumar Kungiyar Africa kuma ana ganin watakila za ta koma gida ne domin neman takaran hawa kujeran tsohon mijinta na shugabancin kasar Africa at Kudu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.