Isa ga babban shafi
Rwanda

Mpayimana zai kalubalanci Kagame a zaben Rwanda

Daya daga cikin ‘Yan adawar Rwanda Philippe Mpayimana wanda ya yi gudun hijirar dole ya dawo a yau Asabar tare da sanar da kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa da za a gudanar a watan Agustan 2017.

Dan Jarida kuma dan adawa a Rwanda Philippe Mpayimana
Dan Jarida kuma dan adawa a Rwanda Philippe Mpayimana youtube
Talla

Mpayimana wanda dan jarida ne ya fara guduwa zuwa Congo Brazaville, daga nan kuma ya tsallaka zuwa Kamaru kafin ya gudu zuwa Faransa a 2003.

Yanzu shi ne dan takara na uku a zaben Rwanda bayan Frank Habineza mai adawa da shugaba Paul Kagame da ya kudiri yin tazarce bayan sauya kundin tsarin mulki a watan disemba.

Akwai dai ‘yan adawa da dama da ke gudun hijira daga Rwanda saboda gudun dauri a gwamnatin Kagame

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.