Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Lagos za ta haramta motocin Damfo

Gwamnatin Lagos na shirin haramta amfani da motocin daukar fasinja da ake kira Damfo, domin rage yawan cunkusu da go-slow da ake samu a birnin, babbar cibiyar kasuwancin Najeriya.

Motocin Damfo na haddasa go-slow a Lagos
Motocin Damfo na haddasa go-slow a Lagos Getty Images/McClatchy-Tribune
Talla

Gwamnan Lagos Akinwumi Ambode ya ce yanayin motocin bai dace da birnin Lagos ba, wadanda kirar Volkswagen ne da babu komi a jikinsu sai karfe.

Motocin Damfo sun kasance hanya mafi sauki da ake gane birnin Lagos a hoto ko a bidiyo wadanda ke jigilar fasinja a sassan birnin.

Saboda karfin motocin na Damfo ba su jin tsoron su daki motar wani akan hanya.

Ambode ya ce zai soke amfani da motocin kafin karshen shekarar nan tare da musanya su da na zamani.

Gwamnan ya ce suna son tabbatar da tsarin sufuri na zamani kafin watan Disemban bana domin kara jan hankalin masu yawon bude ido da zai ba Jihar bkarin kudaden shiga.

Sai dai kafin soke amfani da motocin sai gwamnati ta samar da makoma ga ‘yan Damfon domin barazanar tsaro da magance matsalar rashin ayyukan yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.