Isa ga babban shafi
Gambia

Gambia ta samu tallafi daga Tarayyar Turai

Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da ba kasar Gambia taimakon kudin euro miliyan 225, bayan shugaba Adama Barrow ya yi gargadin cewa kasar ta talauce saboda almubazzaranci da tsohuwar gwamnati Yahya Jammeh ta yi.

Shugaban kasar Gambia Adama Barrow a birnin Banjul.
Shugaban kasar Gambia Adama Barrow a birnin Banjul. REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

Matakin yana a matsayin sabunta taimakon da kungiyar tarayyar tura ke bawa Gambian a baya, makwanni kadan bayan ficewar tsohon shugaba Yahya Jammeh.

A shekara ta 2014 tarayyar turan ta dauki matakin janye tallafin da take bawa kasar, sakamakon haramta alaka ko auren jinsi guda a waccan lokacin.

Jim kadan bayan kammala taron da yayi da shugaba Adama Barrow, Kwamishinan sashin lura da kyautata cigaban alakar kungiyar tarayyar turan da kasashen duniya, Neven Mimica, ya ce za’ayi amfani da tallafin kudin wajen bunkasa noma, gina hanyoyi, da kuma samar da ayyukan yi a Gambia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.