Isa ga babban shafi
Ghana

Gwamnatin Ghana na fatarar motocin hawa

Gwamnatin kasar Ghana ta kaddamar da wani kwamiti na musamman domin gano motoci sama da 200 da ake zargin Jami'an tsohuwar gwamnatin John Dramani sun sace, wadanda ya kamata shugaba Nana Akufo-Addo ya samu bayan rantsar da shi.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo REUTERS/Luc Gnago
Talla

Kakakin Gwamnatin Eugene Arhin ya fadawa manema labarai a birnin Accra cewa yawancin motocin Gwamnati an yi gaba da su.

A cewar Arhin, mota daya kacal kirar BMW Shugaban ke amfani da ita da aka saye shekaru 10 da suka gabata lokacin da Ghana ta yi bikin cika shekaru 50 da samun ‘yancin kai.

Sannan kakakin gwamnatin ya ce fadar shugaban kasar ta iske motoci 74 daga cikin 196 da ya kamata ace gwamnatin Akufu-Addo ta iske.

Jami’an gwamnatin John Dramani Mahama ne dai ake zargi da mallake motocin bayan ya sha kaye a zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Disemba.

Har yanzu dai Jam’iyyar tsohon shugaban ba ta mayar da martani ba akan batan motocin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.