Isa ga babban shafi
Libya

Libya ta nemi taimakon NATO

Kungiyar tsaro ta NATO ta ce Libya ta nemi taimakonta wajen karfafa tsaron kasar, tare da gina ma’aikatun tsaro, hadi da cibiyoyin horar da jami’an tsaronta. Sakataren NATO Jens Stoltenberg, wanda ya sanar da bukatar Libyan yayin jawabi a hedikwatar kungiyar da ke Brussels, ya ce a shirye suke su taimakawa kasar.

Libya ta kasa samun zaman lafiya tun kawar da Ghaddafi
Libya ta kasa samun zaman lafiya tun kawar da Ghaddafi REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Sai dai Mista Stoltenberg bai bayyana lokacin da za su shiga Libya ba.

A yau 17 ga watan Fabrairu ake cika shekaru shida da kaddamar da zanga-zangar da ta kawo karshen gwamnatin Kanal Ghaddafi a 2011.

Kungiyar NATO ce kuma ta taimakawa ‘Yan tawaye wajen yakar gwamnatin Ghaddafi har zuwa mutuwar shugaban da ya shafe shekaru 44 yana mulki a kasar.

Amma an kasa samun zaman lafiya tun kawar da Ghaddafi, inda yanzu aka samu gwamnati biyu da ke wanzar da shugabanci a Tripoli da kuma gabashin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.