Isa ga babban shafi
Gambia

Bikin kaddamar da Adama Barrow A Banjul

A kaddamar da shugaban Gambiya Adama Barrow a hukumance a Banjul babban birnin kasar.Ranar 18 ga watan Febrairu ya zo daidai da ranar da kasar ke cika shekaru 52 da samun yancin kai.

Shugaban kasar Gambia Adama Barrow
Shugaban kasar Gambia Adama Barrow
Talla

Dubban mutane ne suka halarci bikin ciki har da shugabanin wasu kasashen Duniya.

A watan da ya gabata ne aka rantsar da shugaban a ofishin jakandancin Gambiya da ke kasar Senegal bayan da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya ki sauka daga mulki duk da kayen da ya sha a zaben shugabancin kasar da aka gudanar.

Daruruwan al’ummar Gambiya sun tsere daga kasar saboda kaucewa tashin hankali sakamakon rikicin zaben kasar da ya biyo bayan kememen da Jammeh ya yi akan karagar mulki.

Daga bisani dai kasashen Tarrayar Afrika sun yi nasarar warware rikicin cikin ruwan sanyi inda har suka yi nasarar lallamar Jammeh har ya amince da barin kasar zuwa Equatorial Guinea.

Adama Barrow shine shugaban kasa na uku a tarihin kasar ta Gambiya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.