Isa ga babban shafi
Najeriya-Kamaru

Kamaru ta kori 'yan Najeriya sama da 500

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace hukumomin Kamaru sun kori ‘yan Najeriya 500 da suka samu mafaka a kasar sakamakon hare haren kungiyar Boko Haram.

Wasu 'yan gudun hijira da suka tserewa rikicin Boko Haram a sansanin Minawao da ke kasar Kamaru a ranar 25 ga watan Fabarairu, 2015
Wasu 'yan gudun hijira da suka tserewa rikicin Boko Haram a sansanin Minawao da ke kasar Kamaru a ranar 25 ga watan Fabarairu, 2015 today.ng/AP
Talla

Kwamishinan kula da ‘yan gudun hijirar ya bayyana takaicin sa kan yadda hukumomin kasar suka kori mutane 517 cikin su harda 313 da suka nemi mafakar siyasa.

Hukumar tace tana kokarin ganin ta sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakanin gwamnatocin kasashen biyu ranar 2 ga watan gobe, wanda zai bai wa ‘yan gudun hijirar Najeriya 85,000 damar komawa gida.

Bincike ya nuna cewa zuwa ranar 17 ga watan Fabarairu sama da ‘yan Najeriya 61,000 ne ke zaune a sansanin yan gudun hijira na Minawao da ke arewa maso gabashin kasar Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.