rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Burkina Faso Fina-Finai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Fim din Senegal "Felicite" ne gwarzon fim a Afrika

media
Fim din Félicité na Alain Gomis a Senegal Jour2fête

Fim din "Felicite" da ya bayar da labarin wata mawakiya da ta ci karo da waharhallu a rayuwarta shi ya lashe kyautar zinari a gasar nuna fina-finan Afirka FESPACO karo na 25 da aka kammala a birnin Ouagadougou na Burkina Faso.


Wanda ya tsara fim din na "Felicite" daga kasar Senegal Alain Gomis shi ya lashe kyautar zinari.

Wannan na zuwa bayan Fim din ya lashe azurfa a gasar finafinai da aka gudanar a Berlin na Jamus.

Bayan lashe kyautar Alian Gomis ya bayyana farin cikinsa inda ya ce wannan tukuici ne da ya zo a ba-zata, kuma karo na biyu da ya samu tukuicin sakamakon kokarinsa.

Fim din kasar Benin na "Un Orage Africain" ne ya lashe azurfa wanda ya bayar da labarin kyamar mulkin mallaka.

Fim din kasar Morocco na Said Khallaf ya lashe tagulla a gasar nuna finafinan a Ougadougou.