Isa ga babban shafi
Najeriya

Za a kashe N5b ga aikin gyaran tashar jirgin saman Abuja

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta kashe sama da Naira biliyan 5 ga aikin gyaran tashar jiragen saman Abuja da aka rufe har sai an kammala gyara musamman titin da jirage ke tashi da sauka.

Hadi Sirika, Ministan kula da sufurin jiragen sama a Najeriya
Hadi Sirika, Ministan kula da sufurin jiragen sama a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Sannan za a kwashe watanni shida ana gudanar da aikin gyaran filin jirgin, kamar yadda Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya shaidawa manema labarai.

Sai dai Ministan ya ce makwanni shida za a yi ana aikin titin jirgin da ke matukar bukatar gyara.

03:03

Ministan sufurin jiragen sama a Najeriya Hadi Sirika

Bashir Ibrahim Idris

Gwamnati dai ta karkatar da harakokin sufurin jiragen Abuja zuwa Kaduna, da ke da nisan kilomita kusan 200 da birnin na Tarayya.

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce ta dauki matakan tsaro tashar jiragen saman Kaduna da kuma hanyar Kadunan zuwa Abuja domin tabbatar da kare lafiyar matafiya da ke zuwa kasar ta hanyar jiragen sama.

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan kasar Ibrahim Idris ya shaidawa wakilin RFI Hausa a Kaduna Aminu Sani cewa sun girke jami’an ‘yan sand a fannoni da dama don tabbatar da tsaro.

Wasu jiragen kasashe waje da ke jigila a Abuja sun sanar da cewa ba za su je Kaduna ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.